ABNA24 : Shugaba Magufuli ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a jiya Laraba a garinsa na haihuwa wato Chato da ke arewa maso yammacin Tanzaniya inda ya ce: Rigakafin nan na da hatsarin gaske. Idan da a ce waɗannan fararen fatan za su iya yin wani rigakafi, to da kuwa sun yi rigakafin cutar AIDS, tarin fuka da kuma malariya, haka nan da kuma rigakafin cutar cancer.
Duk da cewa dai shugaban ƙasar bai kawo wata hujja don tabbatar da wannan ikirari na sa ba kan wannan rigakafin da ake ci gaba da yinsa a sama da ƙasashe 50 na duniya ba, to amma dai ya buƙaci ma’aikatar lafiya ta ƙasar da ta yi taka tsantsan da rigakafin da aka yi su daga ƙasashen waje.
Shugaba Magufulin dai ya jima yana sanya alamun tambaya kan cutar ta COVID-19 wacce a halin yanzu ta kashe sama da mutane miliyan biyu a duk faɗin duniya, don haka ne ma yake kiran mutane da su dage da addu’oi kawai wajen kare kansu daga cutar ta coronavirus.
342/